Hukumar EFCC ta tsare wasu kwamishinonin guda biyu na hukumar kula da aikin hajji ta kasa NAHCON, bisa zarginsu da aikita laifin zamba.
Cikin wadanda hukumar ta EFCC ta tsare sun hada da kwamishina mai kula da harkokin ma’aikata Aliu Abdulrazak da kuma daraktan kudi na hukumar ta NAHCON Aminu Y. Muhammed.
Rahotanni sun ce dukkan jami’an biyu sun amsa gayyatar zuwa hedkwatar hukumar EFCC da misalin karfe 11 na safiyar ranar Litinin din nan.
Hukumar EFCC na binciken badakalar kudi sama da naira biliyan 50 karkashin jagorancin shugaban hukumar Farfesa Abdullahi Saleh Usman.
A wani taron bita da hukumar ta NAHCON ta gudunar a babbar birnin tarayyar Abuja ya tabo wasu batutuwa guda 16 wanda suke da alaka da cin hanci da rashawa kai tsaye da kuma zamba a cikin harkokin kudi, wanda a yanzu hukumar EFCC na binciken kan su.
Har kawo zuwa wannan lokacin dai hukumar kula da aikin hajjin ta kasa NAHCON tace komai ba dangane da wannan batun.
