
Hukumar Karbar Korafe-Korafe Da Yaki Da Cin Hanci Ta Jihar Kano (PCACC) ta kaddamar da bincike kan zargin karkatar da Naira biliyan 4 mallakar gwamnatin Kano zuwa aikin Kamfanin Dala Inland Dry Port.
Binciken ya biyo bayan korafe-korafen da suka nuna cewa hannun jarin kashi 20 cikin 100 na jihar a aikin an sauya mallakarsa zuwa iyalin tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje.
Rahotanni sun nuna cewa karkatarwar ta faru ne a shekara a 2020 lokacin da aka mayar hannun jarin jihar mallakar wani kamfani mai zaman kansa abin da ya fitar da jihar Kano daga cikin masu mallakar hannun jarin a aikin gaba ɗaya.
Shugaban hukumar, Saidu Yahya ya tabbatar da lamarin, yana mai cewa an fara binciken ne bayan karɓar koke-koke daga ‘yan jihar.
“An gayyaci wasu mutane masu ruwa da tsaki domin yi musu tambayoyi, inda aka kama mutum ɗaya wanda daga baya aka bayar da belinsa bayan ya bayar da bayanai masu muhimmanci”. In ji shi.
Aikin tasahar tsandauri ta Dala, an kaddamar da shi ne domin zama cibiyar jigilar kaya da kasuwanci ga jihohin Arewa, ya zama abin tattaunawa tun bayan da aka ruwaito jihar kano ta rasa hannun jarinta ta wata hanyar da ke cike da zargi