
Gwamnatin Kano tayi gargadin cewar, za ta fara amfani da dokar da kundin mulkin Najeriya ya tanada, domin hukunta iyaye da wakilan yaran da suke bijirewa wajen yiwa ‘ya’yan su alluran rigakafin cututtuka a jihar.
Kwamishinan lafiya na Kano Dr Abubakar Labaran Yusif ne yayi gargadin, gabanin kaddamar da gaggamin yin rigakafin cututtukan kyanda da kyanda bi iska a jihar.
Dr Labaran yace cutukan biyu na kyanda da kyanda bi iska suna da matukar hadari, musamman kyanda bi iska wadda ba’a fiya sanin yara ko mata masu ciki suna dauke da ita ba saboda yadda take zuwa ta tafi cikin sauri, sai dai tana haifar da cututtuka irin su makanta, kurumta, ciwon zuciya da tabin hankali idan ta kama yara ko mata masu juna biyu.
Kwamishinan yace gwamnatin Kano yanzu haka ta dukufa sosai wajen yakar mabanbantan cututtuka ta hanyar matsa lamba a fannin yin rigakafin su wanda haka ne kadai hanyar samar da al’umma mai cikakkiyar lafiya.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa, a wannan karon ana sa ran yiwa yara sama da miliyan 7 daga sabuwar haihuwa zuwa shekaru 15 rigakafin, inda ake saka ran kakkabe cutukan biyu daga Kano daga yanzu zuwa shekara ta 2030.