Rundunar ’Yan Sanda ta kasa ta ɗora laifin ɓacewar bindigo 3,907 a hannun jami’anta a kan sakaci da kuma ƙarancin iliminsu game da kula da makamai.
Kakakin rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi ya bayyana cewa, ɓata-gari ne suka yi awon gaba da bindigogin da ake magana a kai.
Rundunar ta ɗora laifin ci gaban matsalar batn makaman a kan abin da ta kira “sakacin” manyan jami’ai wajen tura ’yan sandan da ba su san ciwon kansu ba wajen aiki.
Ta kuma bayyana takaicinta ne a wata takardar cikin gida da ta fitar, yayin da Majalisar Dattawa take gudanar da bincike kan rahoton Babban Mai Binciken Kudi na Tarayya da ya nuna manyan bindigon ’yan sanda 3,907 sun ɓace.
Aminiya ta rawaito cewa, rahoton kuma ya yi zargin cewa akwai aringizo a adadin da rahoton Babban Mai Binciken Kuɗin ya bayar na bindigogin da suka ɓace.
