
Shugaban kungiyar iyayen yaran Kano da aka sace Kwamared Isma’ila Ibrahim Muhammad ya sanar da da cewa sun sake gano yara 8 ‘yan asalin jihar Kano da aka sace a jihar Delta.
Wannan na zuwa ne daidadi lokacin da ake ci gaba da fadada bincike kan batan sama da yara 100, a cikin shekaru 5 da suka wuce.
Da yake ganawa da manema labarai Shugaban kungiyar Kwamared Isma’ila Ibrahim Muhammad, ya yi ki ga iyayen yaran da su ziyarci hukumar NAPTIP domin tanatacewa ko da Yaransu a cikin 8 din da aka gano a yanzu.
Kwamared Isma’ila Ibrahim Muhammad, ya yi fatan gwamnati za ta ci gaba da ba su gudunmawa ta bangaren binciko sauran yaran da suka bata.
Ko a kwanakin baya ma an samu nasarar gano sama da yara 20, wadanda aka yi safararsu zuwa kudancin kasar nan tare da sauya musu sunaye da addini.