
Ƙungiyar ƙwadago ta ma’aikatan dakon man fetur da iskar gas ta kasa, NUPENG ta dakatar da yajin aikin da ta shirya bayan cimma matsaya da kamfanin mai na Dangote kan ’yancin mutane na kafa ƙungiya.
Wanne na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da NUPENG ɗin ta fitar a shafinta na X.
Cimma matsayar ya biyo bayan ganawa ta musamman da hukumar DSS ta kira, tare da halartar Ministan Kuɗi, Wale Edun, da shugabannin NLC da TUC.
A cikin yarjejeniyar da aka sanya hannu, an amince cewa ma’aikatan kamfanin da ke son shiga ƙungiya za su samu damar yin hakan, tare da fara tsarin nan take da kuma kammala shi cikin makonni biyu.
a cewar yarjejeniya, babu wani ma’aikacin Dangote da za zalunta saboda sanarwar yajin aikin.
Da wannan matsaya, NUPENG ta dakatar da yajin aikin da ta shirya gudanarwa, yayin da ɓangarorin biyu za su koma wurin Ministan Ƙwadago bayan mako guda domin bayar da rahoto.