
Al’ummar unguwar Kuntau da ke Ƙaramar Hukumar Gwale a Jihar Kano, sun shiga jimami bayan rasuwar wani matashin limami mai suna Salim Usman, wanda ake zargin ya rasu a hannun ’yan sanda.
An kama Salim Usman mai kimanin shekaru 24 a gidansa a ranar 22 ga watan Satumba, jim kaɗan bayan jagorantar sallar Magariba, bisa zarginsa da siyan buhun fulawa wadda ake zargin ta sata ce a shakarar data wuce.
Mahaifin matashin Sheikh Adam Usman ya shaidawa Aminiya cewa, bidiyon na’urar CCTV ya nuna yadda jami’an ’yan sanda biyu suka yi wa ɗansa dukan tsiya a lokacin da suka zo su kama shi.
“An ci gaba da dukansa a ofishin ’yan sanda, wanda hakan ya yi sanadin mutuwarsa”. In ji mahaifin Usman
Sannan ya ce, tuni suka kai ƙara hukumar ’yan sanda, kuma an shaida musu cewa an kama wasu jami’ai bisa zargin rashin ƙwarewa a aikinsu, ana kuma gudanar da bincike.
Tuni dai aka bayar da gawar Salim Usman a ranar Juma’a domin a binne shi bayan kotu ta bayar da umarnin a yi gwaji a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano.