
Ya ware kudin ne daga aljihunsa domin su koyar a makarantun Islamiyya da na Firamare da kuma Sakandare a karamar Hukumar Bichi.
Dan Majalisa mai wakiltar Karamar Hukumar Bichi a karkashin Gidauniyar Kabiru Abubakar Bichi ne ya dauki malam sannan da kuma wasu karin 200 don gudanar da wannan aiki a duk fadin karamar hukumar Bichi.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Jamilu Halliru Master, Babban Daraktan Yada Labarai na Dan Majalisar ya fitar a rana Lahadi.

“Tun a ranar 10 ga watan Oktobar 2024 dan majalisar Tarayya Honorabul Dakta Abubakar Kabir Abubakar ya bayar da umarnin sake daukar sabbin malamai masu hazaka su 200 saboda karancin malamai da ake fama da su a Karamar Hukumar Bichi”. In ji shi
Jimlar mata 196 mata 122 ne ya dauka, an kasafta su kamar haka
A. Islamiyya 50 (Maza 42, Mata
B. Primary 130 (Maza 64, Mata 66)
C. Upper Basic 98 (Maza 63, Mata 35)
D. Senior Secondary School 40 (Maza 27, Mata 13)
