Saurari premier Radio
34.9 C
Kano
Thursday, April 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoZamu hukunta jagororin APC na Kano sabida faduwa zabe- Abdullahi Adamu |...

Zamu hukunta jagororin APC na Kano sabida faduwa zabe- Abdullahi Adamu | Premier Radio | 05.04.2023

Date:

Jam’iyyar APC ta ce faduwar ta a zaben gwamnan Kano ba zai rasa nasaba da son zuciyar wasu yayanta dake jihar ba.

Shugaban jam’iyyar na kasa Abdullahi Adamu ne ya bayyana hakan a zantawarsa da kafar BBC Hausa.

Yace tabbas lamarin abin takaici ne, amma duk da haka lokaci bai kure ba na jan kunnen kusoshin APCn kan su yi abin da ya kamata.

Har ila yau, bayan kammala hidindimun zaben, Adamu yace zasu bi Kadin yadda abubuwa suka kasance, da kuma daukar mataki daidai ruwa daidai tsaki.

Game da zabe shugaban kasa da jam’iyyar ta APC tayi nasara, Adamu yace dama haka suka yi tsammani, kuma abinda ya faru kenan.

Sannan ya bayyana kwarin gwiwar sa cewa jam’iyyar ce zata yi nasara a zabukan cike gurbi na gwamnoni da yan majalisa dake tafe.

A zaben na shugaban kasa dai, jam’iyyar NNPP ce ta sami kuri’u mafi rinjaye fiye da sauran a Kano, wadda ta tsayar da tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Kwankwaso a matsayin dan takara.

Har ila yau, APC ta sha kasa a zaben gwamna da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris din da ya gabata, inda tazo ta biyu da kuri’u 890,705, yayinda NNPP mai kayan marmari ta lashe zaben da kuri’u 1,019,602.

Wannan ne ya baiwa Abba Kabir Yusuf nasarar zama gwamnan jihar mai jran gado.

Bayan shan kayin, dan takarar APC a zaben na gwamna, Dr. Nasiru Gawuna, ya bayyana karbar kaddara, tare da fatan alkhairi ga Abba.

To sai dai daga bisani, jam’iyyarsa ta yi watsi da kalaman nasa, inda ta sha alwashin garzayawa kotu.

Latest stories

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Farashin Dizel ya koma 1000 a Najeriya

Rahotanni sun bayyana matatar mai ta Dangote ta sanar...

Related stories

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Daurawa ya sauka daga mukaminsa na babban kwamandan Hisbah

Sheikh Daurawa ya sauka daga mukaminsa na babban kwamandan...