Saurari premier Radio
27.9 C
Kano
Friday, April 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiSiyasaZABEN 2023: INEC tace ta samu kudin da take bukata | Premier...

ZABEN 2023: INEC tace ta samu kudin da take bukata | Premier Radio | 22.02.2023

Date:

Yayin da ya rage kwanaki uku a gudanar babban zaben kasar nan, hukumar zabe ta kasa INEC ta sanar da samun takaddun kudaden da ta bukata daga babban bankin kasa CBN don gudanar da babban zaben.


Da yake shaidawa jaridar Daily Trust hakan a daren jiya Alhamis, daya daga cikin kwamishinonin hukumar zaben da ba’a bayyana sunansa ba, yace an bai wa shugabannin rassan CBN umarnin su bai wa ofisoshin INEC a jihohi kudaden da suke bukata.


Kafin wannan lokaci, INEC ta yi fargabar cewa rashin samun kudin zai haifar mata cikas wajen gudanar harkokinta yadda ya kamata.


INEC ta fuskanci jinkiri wajen samun kudaden ne sakamakon sabbin dokokin da CBN ya samar, na takaita ta’ammali da takaddun kudi a hannun da kuma sauyin takardun kudin.


Yayin ziyarar da shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, ya kaiwa gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya nuna cewa sun fi bukatar tsabar kudi maimakon turawa ta banki don su samu damar aiwatar da ayyukansu yadda ya dace.

Latest stories

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Farashin Dizel ya koma 1000 a Najeriya

Rahotanni sun bayyana matatar mai ta Dangote ta sanar...

Related stories