Saurari premier Radio
23.8 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiWani sansanin sojan Isra'ila ya zama cibiyar azabtar da Falasdinawa a hamadar...

Wani sansanin sojan Isra’ila ya zama cibiyar azabtar da Falasdinawa a hamadar Negev.

Date:

Wani rahoto ya bayyana wani yanayi mai tayar da hankali a sansanin hamadar Sde Teiman, wani sansanin sojan Isra’ila da ya zama cibiyar azabtar da Falasdinawa a hamadar Negev.

Rahoton ya fallasa bayanan sirrin Isra’ila na yadda ake tsare Falasɗinawan da ta kama lokacin da ta kutsa yankin Gaza da ta yi wa ƙawanya.

Masu fallasar, waɗanda ke fuskantar hukuncin shari’a da ramuwar gayya daga ƙungiyoyi masu goyon bayan munanan manufofin Isra’ila a Gaza, sun ce fursunonin da ake tsare da su na cikin matsanancin hali da ɗimauta.

Rahoton ya ce wasunsu na wani ɗakin mai kamar na asibitin, inda aka ɗaure wadanda suka ji rauni jikin gadajensu, an sanya musu ƙunzugun zamani, wato famfas, ana basu abinci ta cikin wani ɗan kwaroron roba.

An lura cewa, an ba masu gadi umarnin rufe bakin fursunonin, su kuma ware wadanda ke bayar da matsala domin kara hukunta su.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...