Saurari premier Radio
23.5 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin tarayyaShugaban kungiyar malaman jamio’in, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya bayyana damuwa kan hanyoyin...

Shugaban kungiyar malaman jamio’in, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya bayyana damuwa kan hanyoyin da aka bi wajen nada yan siyasar.

Date:

Kungiyar malaman jamio’i ta kasa ASUU ta kalubalanci matakin gwamnatin tarayya na nada yan siyasa a matsayin shugabannin gudanarwar jami’oin kasar nan.

Shugaban kungiyar na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke ne ya bayyana hakan a ganawarsa da jaridar Tribune, yana mai bayyana damuwa kan hanyoyin da aka bu wajen nada yan siyasar.

A baya-bayan nan ne dai gwamnatin tarayya ta sanar da nada wasu yan siyasa a matsayin shugabannin gudanarwar jami’ionta da kwalejojin ilimi da na fasaha.

A nan Kano dai an nada dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna, a matsayin shugaban kwamitin gudanarwa na jami’ar Bayero.

Da yake yiwa Premier Radio karin bayani kan kalubalanatar nade-naden, shugaban ASUU a shiyyar Arewa maso yamma, Farfesa Abdulkadir Dambazau, ya ce matakin ba zai haifar da da mai ido ba, saboda haka yake ganin akwai bukatar shugaban Tinubu ya sake nazari domin hakan zai jefa jamio’in kasar nan cikin sha’anin siyasa.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...