Saurari premier Radio
23.8 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiShugaban jam’iyyar APC na jihar Kano,ya bukaci jami’an tsaro su gaggauta kama...

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano,ya bukaci jami’an tsaro su gaggauta kama shugaban jam’iyyar NNPP na Kasa.

Date:

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas ya bukaci jami’an tsaro su gaggauta kama shugaban jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso akan kallaman da yayi yana zargin gwamnatin tarayya da sa hannu wajen samar da wani sabon salon boko haram a arewacin kasar nan.

Abdullahi Abbas ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar yayin da yake mayar da martani ga kalaman da Kwankwaso a wajen bikin kaddamar da aikin gina titin karkara mai tsawon kilomita 85 a mahaifarsa, Madobi.

Sanarwar ta kara da cewa, shugaban jamiyyar APC yayi kira ga jami’an tsaro da su gaggauta kamo Kwankwaso domin ya tona asirin wadanda ya kira makiyan jihar Kano da ke yi wa gwamnatin tarayya aiki domin haifar da sabon salon ‘yan ta’addan Boko Haram kamar yadda yayi ikirari.

Abdullahi Abbas ya kara da cewa wadannan kalamai na nuni ne da wata muguwar manufa da Kwankwaso da makarrabansa suka yi na kawo tashin hankali a Kano.

A nata bangaren Fadar shugaban kasa ta musanta zarge-zargen da Sanata Kwankwaso ya yi mata na shirin tayar da tarzoma a jihar Kano, musamman ma ayyana dokar ta baci.

Mai magana da yawun shugaban kasar Bayo Onanuga yace ba wani abu cikin kalaman na Kwankwaso illa shaci fadi da babu wata hujja a cikin ta.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...