Saurari premier Radio
24.7 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiShugaba Bola Tinubu ya gana da wani ayari ƙarƙashin jagorancin shugaban jam'iyyar...

Shugaba Bola Tinubu ya gana da wani ayari ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyyar APC mai mulki, Abdullahi Uamar Ganduje a fadar gwamnatin Najeriya da ke Abuja.

Date:

Shugaba Bola Tinubu ya gana da wani ayari ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyyar APC mai mulki, Abdullahi Uamar Ganduje a fadar gwamnatin Najeriya da ke Abuja.
Jaridar Punch ta ambata cewa ko da yake ba a bayyana manufar taron a bainar jama’a ba, amma dai ta fahimci cewa mahalarta sun gabatar da wata maƙala da ta ƙunshi muhimman shawarwari a kan hanyoyin da za a kawo ƙarshen rikicin manoma da makiyaya a faɗin ƙasar.
Jaridar ta ambato wata majiya na cewa taron wanda aka fara da tsakar ranar Alhamis ya buƙaci kasancewar manyan hafsoshin tsaron Najeriya saboda batun ya shafi al’amuran tsaron ƙasa.
Rikicin manoma da makiyaya a Najeriya, ya yi sanadin mutuwar ɗumbin ‘yan ƙasar a kan abincin dabbobi wanda ke daɗa ƙaranci sakamakon gurgusowar hamada da ɗumamar yanayi da bunƙasar jama’a, ke faɗaɗa buƙatun ƙasar noma.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories