ALIYU ABUBAKAR GETSO
Gwamnatin tarayya ta ce tana shirin dakatar da yawan karbar haraji da ake yi kan hanyoyin kasar nan.
Ministan Sufuri Mu’azu Sambo ne ya sanar da hakan yayin taron kungiyar ma’aikatan sufuri a Abuja.
Mu’azu Sambo ya ce yawan karbar haraji da ake yi a hanyoyin kasar nan ya sabawa dokar kungiyar kasashen yammacin Afrika ECOWAS.
Ministan sufurin yace gwamnati za ta kawo gyara a tsarin domin bada damar safarar kayayyaki a kasar nan ba tare da fargabar haraji ba.
Taron dai ya samu halartar masu ruwa da tsaki kan harkar sufuri da suka hadar da jami’an hukumar kiyaye afkuwar hadurra ta kasa FRSC.