Saurari premier Radio
35.9 C
Kano
Wednesday, April 24, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKasuwanciSauyin Kudi: Majalisa na son ganin Emifiele ruwa a jallo | Premier...

Sauyin Kudi: Majalisa na son ganin Emifiele ruwa a jallo | Premier Radio | 27.03.2023

Date:

Ibrahim Hassan Hausawa

 

Majalisar wakilan Najeriya ta umurci babban sufetan ‘yan sandan kasar ya kamo gwamnan babban banki, CBN tare da kai mata shi gaban zauren a ranar Talata mai zuwa.

 

Wannan matsaya da majalisar ta cimma wajen daukar wannan mataki na zuwa ne bayan ta gayyaci gwamnan babban bankin har sau biyu amma ya gaza zuwa.

 

Wani rahoto daga majalisar na cewa ‘yan majalisar suna so ne su ji daga bakin gwamnan dalilin da ya sa ba za a kara wa’adin daina amfani da tsofaffin takardun naira ba, wadanda bankin ya ce za su daina aiki daga ranar 31 ga wannan wata na Janairu.

 

‘Yan majalisar sun fusata ne sakamakon gazawar gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emefiele wajen bayyana a gaban wani kwamiti na musamman da majalisar wakilan ta kafa, kuma har sau biyu suna zaman jiran ya bayyana gaban su, amma kuma gwamnan bankin yaki zuwa ko kuma tura wakili.

 

Kazalika kwamitin ya gana da shugabannin bankunan kasuwanci da ke Najeriya, duka dai da nufin jin ta bankin su inda gaskiyar maganar take game da karancin da ake fama da shi na sabbin takardun kudin.

Latest stories

Related stories

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...