Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Tuesday, April 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKasuwanciSauyin fasali: Tsaffin takardun kudi sun fara wadata | Premier Radio |...

Sauyin fasali: Tsaffin takardun kudi sun fara wadata | Premier Radio | 26.03.2023

Date:

Rahotanni na nuna cewar babban bankin kasa CBN ya kara wadata bankunan yan kasuwa da tsaffin takardun kudi, don kawo karshen karancin takardun tsakanin jama’a

 

Wannan ya biyo bayan umarni na musamman da CBN ya baiwa bankunan kan cigaba da aiki har a ranakun karshen mako.

 

A Asabar din da ta gabata, Premier Radio ta rawaito yadda wasu bankunan a sassan jihar Kano suka bijirewa umarnin.

 

To sai dai a jiya Lahadi, yawancin bankunan sun fito.

 

Zuwa yanzu, matsalar karancin kudin ta fara zuwa karshe a tsakanin jama’a, ganin yadda samun su yayi matukar sauki musamman a kasuwanni.

 

Sabanin yadda bankunan suka kayyade adadin takardun kudin da suke baiwa abokan hulda a rana zuwa dubu 5, a yanzu, mutum guda ya kan iya samun sama da naira dubu 20.

 

Tun bayan bijiro da shirin suya fasalin kudi da gwamnatin taraya ta yi, aka fara samun matsalar karancin kudin.

 

Daga cikin manufofin billo da shirin sun hadar da bunkasa tsarin hada hadar kudi ta Internet, dakile bazuwar yagaggu da jabun kudi, yaki da cin hanci, da kuma lalata kudin da masu garkuwa da mutane suka tara.

 

Bisa ga yadda shirin yazo a kakar siyasa, an kai ruwa rana, game da yadda lamarin yayi tasiri wajen dakile sayen kuri’u  lokacin zabe.

 

Batun ya kai ga billar cece kuce tsakanin jam’iyyun  siyasa, inda wasu yan takarar suka yi zargin an billo da shirin ne musamman domin kawo wa nasarar su cikas.

 

 

 

Latest stories

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Related stories