Saurari premier Radio
23.5 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiSaudiyya ta fara koro maniyyatan kasar nan wadanda basu da takardun izinin...

Saudiyya ta fara koro maniyyatan kasar nan wadanda basu da takardun izinin aikin Hajji.

Date:

Hukumomin Saudiyya sun fara koro maniyyatan kassar nan wadanda basu da takardun iznin aikin Hajji a bana.

Ma’aikatar harkokin musuluncin kasar ta sanar da cewa gwamnatin Saudiyya na kuma cin tarar Naira milyan uku da dubu dari tara ga maniyyata marasa takardun da suka saba dokokin aikin Hajjin.

Sanarwar ta kara da cewa ana kamen marasa takardar iznin aikin Hajjin a birnin Makkah, da Mina, da Arafa, da Muzdalifa, da cibiyoyin tantance alhazai, da tashoshin jirgin kasa, da shingayen binciken jami’an tsaro, da wasu muhimman wurare.

Ma’aikatar aikin hajjin ta ce an rabawa maniyyata katin shaida domin saukaka musu zirga-ziraga, yayin da za a ci gaba da kamen har zuwa ranar 20 ga watan nan na Yuni.

A halin da ake ciki kuma, duk wanda aka kama da laifin safarar maniyyata marasa takardun iznin aikin Hajji, za su fuskanci daurin wata shida, da tarar Riyal dubu hamsin, hadi da kwace abun hawansu.

Wadanda ba ’yan Saudiyya ba kuma, za a kora su zuwa kasarsu, sannan a haramta musu shiga Saudiyya na wani lokaci.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...