Saurari premier Radio
23.5 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin tarayyaRunudunar sojin saman Najeriya, ta sanar da shirinta sayo sabbin jiragen yaki...

Runudunar sojin saman Najeriya, ta sanar da shirinta sayo sabbin jiragen yaki 50 nan da shekara mai zuwa.

Date:

Runudunar sojin saman Najeriya, ta sanar da shirinta sayo sabbin jiragen yaki 50 nan da shekara mai zuwa, a wani mataki na karfafa ayyukan yaki da ‘yan ta’adda da take yi, musamman a yankin arewa maso gabashin Najeriya da ma sauran sassan kasar.

Babban hafsan rundunar sojin saman kasar, Marshal Bala Abubakar, ne ya bayyana hakan, yayin kaddamar da sabbin ayyuka a sansanin sojin saman wato ‘Forward Operational Base 213’, da ke jihar Katsina.

Sabbin ayyukan sun hada da titin mota da wuraraen ajiye jiragen sama guda biyu, sai filin wasan kwallon kaf ana zamani da kuma sauran wasu gine-gine.

Ya kuma yabawa gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi da kuma jami’an rundunar Sojin sama, bisa kokarin da suke yi a ayyukan yaki da ta’addanci domin wanzuwar zaman lafiya a kasar.

 

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...