Saurari premier Radio
23.5 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiRundunar sojin kasar nan ta karyata zargin da ake mata na daukar...

Rundunar sojin kasar nan ta karyata zargin da ake mata na daukar ma’aikata.

Date:

Rundunar Sojin kasar nan ta ƙaryata wani rahoto da ake yaɗawa a shafukan intanet wanda ke cewa tana ɗaukar masu ikirarin jihadi aiki a ƙasar.

An yi ta yada wani bidiyo a shafukan sada zumunta, inda ake zargin hukumomin sojin kasar da daukar ‘yan ta’adda musamman wadanda ke da alaka da ISIS da sauran kungiyoyin ta’addanci na duniya cikin rundunar.

Mai magana da yawun rundunar, Onyema Nwachukwu, a martanin da ya mayar, ya ce labarin kamar yadda aka bayyana a cikin faifan bidiyon ba gaskiya ba ne.

Rundunar soji ta nemi ‘yan Nijeriya da su yi watsi da rahoton wanda ta ce an ƙirƙire shi ne ba tare da sanin dokokin aikinta ba. Sannan ta jaddada aniyarta na ci gaba da kare rayukan ‘yan Nijeriya da bin dokokin aikinta ka’in da na’in.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...