Saurari premier Radio
23.8 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiNetanyahu ya nanata ƙudirin sojojin Isra'ila na kai farmaki ta ƙasa a...

Netanyahu ya nanata ƙudirin sojojin Isra’ila na kai farmaki ta ƙasa a Rafah.

Date:

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya nanata kudirin sojojin Isra’ila na kai farmaki ta kasa a Rafah, ko da anyi sulhu da Hamas, ko akasin haka.

Ya ce, sojojin Isra’ila za su shiga Rafah domin kawar da ayarin dakarun Hamas.

Sanarwar da ofishin Firaministan ya fitar, ta ce tilas ne a kwato dukkan Yahudawan da suka rage a hannun Hamas, wadanda ta yi garkuwa da su ranar 7 ga watan Oktobar bara.

Wani babban jami’in Isra’ila da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaidawa manema labarai cewa, gwamnati za ta jira har zuwa daren yau Laraba domin jin matakin da Hamas za ta dauka game da batun tsagaita wuta.

Ya kara da cewa, Isra’ila za ta yanke shawara da zarar Hamas ta bayyana matsayinta dangane da shawarwarin da aka cimma a tattaunawar tsagaita wuta da aka gudanar a birnin Al’Qahirar kasar Masar.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...