Saurari premier Radio
34.3 C
Kano
Monday, September 25, 2023
Saurari Premier Radio

Chairman

Alhaji Abba Dabo

Chairman

Each element can be added and moved around within any page effortlessly. All the features you need are just one click away.

Admin Department Members

Engineering Department Members

Marketing Department Members

Muhammad Aminu Jolly

Manager

Muhammad Aminu tsohon ma’aikacin rediyo ne, kwararren injiniya da harkokin mulki da aikin banki da ya samu shahara a gidan Radio Kano 11 FM lokacin da ya ke gabatar da shirin ‘a Jolly Good Show’ inda sunan Jolly ya makale masa. Tsawon shekaru fiye da talatin da ya yi yana aiki, Malam Aminu Jolly ya rike mukamin jami’in kade-kade da tsara` shirye-shirye a Cool/Wazobia FM kafin daga baya ya zama manajan shirye-shirye a Guarantee Radio.

News and Report Department Members

Mukhtar Yahya Usman

Manager

Malam Mukhtar kwararren dan jarida ne,kuma mai fafutukar tabbatar da adalci da ya` shafe shekaru goma yana wannan sana’a. Yana da kyakkyawar hulda da abokan aiki da ma dukkan jama’a. Ya fara aiki a Freedom Radio a shekarar 2012 inda ya samu gogewa sosai har ya kai matsayin shugaban sashen al’amuran kasashen waje. Ya kuma rike mukamin Editan jaridar ‘Kano Focus da ake wallafawa ta intanet. Takardun shaidar ilminsa sun hada da Diploma da digiri na biyu, wato Masters, da ya samu a Jami’ar Bayero, da Northwest University Kano. Ya yi rubuce-rubuce da dama da su ka samu martani kan alkiblarsu bisa wasu manufofin kasar nan.

New Media Department Members

Program Department Members

Political Department Members

Kabiru Garba Haruna Sheka

Manager

Kabiru ya samu shaidar aikin rediyo da daukar hoto daga makarantar koyon aikin jarida ta Gwauron Dutse kafin shiga Jami’ar Bayero inda ya samu babbar Diploma a aikin jarida. Ya fara aiki a Freedom Radio sannan ya koma Vision Radio Abuja inda ya yi aikin shekara biyar a sassa daban daban, daga nan sai aka nada shi manajan shirye-shirye a Progress Radio Gombe kafin daga baya ya koma Prestige Radio Minna a jihar Neja a dai wannan matsayi na manajan shirye-shirye. A watan Disambar 2020 sai Kabiru ya`komo gida Kano domin taimakawa wajen kafa wata sabuwar tashar Rediyo inda nan ma ya rike mukamin manajan shirye-shirye. Ya halarci kwasa-kwasai da dama, ciki har da na BBC Media Action, da PEN University a Lagos, tare da samun horo kan bincike a aikin jarida daga Gidauniyar Mac-Authur da Gidan Rediyon BBC. Kabiru Sheka na daga cikin ‘yan jaridar farko da suka fara aiki a sabuwar tashar Premier Radio a watan Disambar 2021 inda ya fara da mukamin manajan shirye-shirye.