Saurari premier Radio
23.5 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiMatar Shugaban ƙasar Turkiyya Emine Erdogan Na Ziyara Najeriya.

Matar Shugaban ƙasar Turkiyya Emine Erdogan Na Ziyara Najeriya.

Date:

Uwargidan Shugaban Turkiyya Emine Erdogan na wata ziyara a kasar nan don wani gagarumin taro kan wayar da kai dangane da sankara da kuma shirin jan hankalin duniya kan cutar.

Uwar gidan Shugaban kasar nan Oluremi Tinubu ce ta tarbe ta a Abuja, babban birnin Nijeriya.

Kamar yadda Mai Ɗakin Shugaban Turkiyya ta bayyana a cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin X ranar Laraba, tace Akwai ƙarfafa gwiwa ganin irin yadda Nijeriya take ɗaukar nauyin ‘Shirin Wayar da Kai kan Sankara a Ƙungiyar Ƙasashe Musulamai na Afrika’ a bana, inda aka ɗora kan taron da aka yi a Istanbul a 2016 a matsayin wani ɓnagre na Babban Taron Muslunci na 13.

Uwargidan shugaban kasar Turkiyya ta ƙara da cewa, tana fatan taron zai samar da sakamako mai kyau, kuma ta yi imanin cewa hadin kan zai sa a kara wayar da kan jama’a.

A nata bangaren, Uwargidan Shugaban Nijeriya, Oluremi Tinubu ta ce tana fatan sakamakon taron zai kasance mai amfani.

 

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...