Saurari premier Radio
29.1 C
Kano
Monday, July 22, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiMataimakin shugaban ƙasa ya tashi daga Abuja zuwa Dallas na kasar Amurka.

Mataimakin shugaban ƙasa ya tashi daga Abuja zuwa Dallas na kasar Amurka.

Date:

Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya tashi daga Abuja zuwa birnin Dallas na kasar Amurka, domin wakiltar shugaba Bola Tinubu a taron kasuwanci na Amurka da Afirka na 2024 wanda kungiyar kamfanoni kan Afirka ta shirya.

A wata sanarwa da babban mai taimaka nasa na musamman kan harkokin yada labarai Stanley Nkwocha ya fitar, ya ce mataimakin shugaban kasar zai bi sahun sauran shugabannin siyasa da na kasuwanci a fadin Afirka a wajen taron da ke kunshe da manyan batutuwan da za a tattauna da harkokin kasuwanci da kulla kawance a fannonin cinikayya.

Daga cikin shugabannin Afirka da ake sa ran za su halarci taron akwai Shugaba Joseph Boakai na na kasar Liberia; Shugaban kasar Malawi Lazarus Chakwera; Shugaba Joao Lourenco na Jamhuriyar Angola; Shugaba Mokgweetsi E. K. Masisi na Jamhuriyar Botswana; Shugaba José Maria Neves na Jamhuriyar Cabo Verde,
Baya ga taron kolin, ana sa ran Shettima zai yi jawabi a wani taro da zai duba batun zuba jari a fannonin ababen more rayuwa a nahiyar Afirka tare da mai da hankali kan tasiri da samun riba.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...