Saurari premier Radio
23.5 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMajalisar dattawa ta ce gwamnatin tarayya ta manta da yankin arewa maso...

Majalisar dattawa ta ce gwamnatin tarayya ta manta da yankin arewa maso gabas.

Date:

Majalisar dattawa ta ce gwamnatin tarayya ta manta da yankin arewa maso gabas a wasu daga cikin manyan ayyukanta da take yi a fadin kasar nan.

Sanata Muhammad Danjuma Goje daga jihar Gombe ne ya gabatar da kuduri kan wannan batu, wanda kuma ya samu goyon bayan majalisar baki daya.

Sanata Goje ya ce shugaba Tinubu ya dauki matakan gina manyan hanyoyi na zamani a sassa biyar na kasar nan, amma babu ko hanya daya da za ta ratsa yankin arewa maso gabas.

Ya ce Tinubu ya yi alkawarin gina babbar hanya daga Legas zuwa birnin Kalaba da wadda za ta taso daga Legas zuwa Sokoto, sannan ya yi wata daga Kalaba zuwa babban birnin Tarayyar Abuja.

Ya ce ya magantu a zauren majalisa, saboda ya na ganin za a yi wadannan hanyoyi da suka mamaye shiyya biyar amma aka manta da yankin da ya fito.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...