Kotun sauraron korafin zabe dake Kano ta tabbatar da nasarar dan majalisar jiha na NNPP mai wakiltar Bebeji, Hon. Ali Muhammad Tiga.
Kotun karkashin mai shari’a L B Owolaba, tayi watsi da karar da Auwal Ibrahim na APC ya shigar dake kalubalantar kasancewa Ali Muhammad Tiga a matsayin dan jam’iyar NNPP da kuma zargin yin a ringizon kuri’a.
Da yake yanke hukunci mai shari’a L b Owolaba ya ce mai kara ya gaza gamsar da kotu da kwararan hujjoji bisa haka tayi watsi da karar.
