Kotun sauraron ƙarar zaɓen gwamnan jihar Bauchi, ta tabbatar da nasarar Dakta Bala Muhammad (Kauran Bauchi) na jam’iyyar PDP, inda tayi watsi da kalubalantar nasarar sa da jam’iyyar APC da dan takararsu, Air Marshal Sadiq Abubakar, ke masa akan babban zaɓen shekarar 2023.
