Saurari premier Radio
38.9 C
Kano
Friday, March 29, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKotu ta bada belin Mu'azu Magaji, bisa wasu sharuda

Kotu ta bada belin Mu’azu Magaji, bisa wasu sharuda

Date:

Abubakar Haruna Galadanci

Kotun Magistiri dake Nomansland ta bayar da belin tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano, Injiniya Mu’azu Magaji Dan Sarauniya.

Kotun mai lamba 58 ta bayar da belin ne kan naira miliyan daya, tare da gindaya masa wasu sharuda da sai ya cika belin zai bayu.

PREMIER RADIO ta rawaito mai shari’a Aminu Gabari ya ce bayan biyan kudin da Dan Sarauniya zai yi sai ya kuma ajiye fasfo dinsa na tafiya.

Kazalika zai kawo mutum biyu da za su tsaya masa, dole na farko ya zama mai garin kauyen Sarauniya wato kauyen da ya fito, na biyun kuma dole ya zama limamin garinsu ko kuma kwamandan Hizban garin.

A ranar 27 ga watan Janairun da ya gabata ne ‘yan sanda suka kama Injiniya Mu’azu a Abuja.

An kuma mayar da shi jihar Kano inda ‘yan sanda suka gabatar masa da tuhume-tuhumen da ake zarginsa da su, na keta mutunci gwamnan Jihar Abdullahi Umar Ganduje

Latest stories

Related stories