Saurari premier Radio
23.8 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiKashim Shettima ya ƙaddamar da shirin inganta ilimin sakandare.

Kashim Shettima ya ƙaddamar da shirin inganta ilimin sakandare.

Date:

Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, ya ƙaddamar da wani shirin inganta Ilimin sakandare da hukumar raya yankin Arewa maso Gabas ke aiwatarwa, domin shawo kan matsalolin da suke shafar wannan bangare.

Wannan shiri dai na da nufin inganta ilmi, da koyar da sana’o’i ga ɗaliban da suka kammala karatu a makarantun sakandare a jihohin yankin guda shida.

Da ya ke ƙaddamar da shirin a gidan gwamnatin jihar Bauchi, Kashim Shettima ya jaddada muhimmiyar rawar da ilmin sakandare ke takawa a karatun zamani, inda ya ce, tamkar wani tsani ne bayan karatun Firamare.

Ya ce yankin na Arewa Maso Gabas na fama da matsalar ƙarancin shigar da yara makarantun sakandare, amma kuma ya yaba haɗin kai da jajircewar gwamnonin shiyyar wajen inganta yankin.

A jawabinsa, shugaban hukumar ta raya yankin Arewa maso Gabas, Muhammad Alkali, ya ce manufofin shirin sun haɗa da inganta makarantun gaba da sakandare, da bunƙasa sana’o’in hannu, da kyautata ƙwarewar malamai.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...