Saurari premier Radio
23.5 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiKashi 70 Bisa 100 na Yaran da ke Zuwa Makaranta a Najeriya...

Kashi 70 Bisa 100 na Yaran da ke Zuwa Makaranta a Najeriya Basa Fahimtar Darussansu-Rahoto

Date:

Hukumar kula da tsare tsaren ilimi da gudanarwa ta kasa ta bayyana damuwa game da rahoton da ke nuna cewa kashi 70 cikin 100 na yaran kasar nan dake zuwa makaranta ba sa iya fahimtar abin da suke karantawa.

Babban daraktan hukumar, Dr. David Shofoyeke ne ya bayyana hakan yayin da yake bude taron horarwa na mako daya da aka shirya wa shugabannin makarantu su 60 kan tsarin gudanar da makaranta mai tasiri.

Ya ce shirin bunkasa ilimin malamai yana da matukar amfani wajen magance rashin ingancin ilimi, lamarin da ya janyo hukumar ta shirya wannan horaswar a bangaren Arewa Maso Yammacin kasar nan.

Shugaban ya kuma lura cewa kashi 49 cikin dari ne kawai na yara da ke zuwa makaranta ke iya karatu da kuma fahimtar abin da suka karanta.

A bangaren lissafi kuma, ya ce kashi 55 cikin dari ne kawai ke iya lissafi mai sauki.

Wannan bayanin na cikin sakamakon binciken da hukumar auna nasarar koyo ta fitar wanda yake nuni da koma bayan da sha’anin ilimi ke ciki a kasar nan.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...