Saurari premier Radio
29.1 C
Kano
Monday, July 22, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiKasar Ingila ta sha da kyar, inda ta kai wasan kwata final...

Kasar Ingila ta sha da kyar, inda ta kai wasan kwata final a gasar Euro 2024 bayan doke Slovakia da ci 2:1.

Date:

Ƙasar Ingila ta sha ƙyar a hannun Slovakia bayan ta yi nasara da ci 2-1 a wasan zagaye na 16 na Gasar cin kofin nahiyar turai da ake bugawa a ƙasar Jamus.

Ɗan wasan gaban Slovakia, Ivan Schranz ne, ya fara jefa ƙwallo a minti na 25 da fara wasan.

Ingila ta warware ƙwallon ta hannun ɗan wasan gabanta, Phil Foden, amma na’urar VAR ta kashe ƙwallon sakamakon satar gida da ɗan wasan ya yi.

Ingila ta mamaye filin inda ta dinga kai hare-hare, amma sai a minti na 95 ta samu damar warware ƙwallon ta hannun ɗan wasan gabanta, Jude Bellingham.

An tashi wasan da ci 1-1, inda aka tafi hutun ƙarin lokaci na minti 15, wanda a nan ne Harry Kane ya sake jefa wa Ingila ƙwallo ta biyu a raga.

Bayan tashi daga wasan an bai wa Jude Bellingham kyautar gwarzon ɗan wasan da ya fi hazaƙa a wasan.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...