Saurari premier Radio
23.8 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiKamfani a ƙasar Denmark ya amince da zuba jari kan tashoshin jiragen...

Kamfani a ƙasar Denmark ya amince da zuba jari kan tashoshin jiragen ruwa a kasar nan

Date:

Wani kamfanin fito na ƙasar Denmark, A.P. Moller-Maersk, ya amince wajen zuba jarin kudi dala milyan dari shida a tashoshin jiragen ruwan kasar nan.

Kamfanin ya ayyana aniyar zuba jarin ne yayin ganawar da shugaba Bola Tinubu ya yi da shugabansa, Robert Maersk Uggla, a gefen taron kasuwanci na duniya da aka gudanar a birnin Riyadh na Saudiyya.

Shugaba Tinubu, ya ce jarin da kamfanin zai zuba zai ƙarfafa dala milyan dubu ɗaya da tuni aka sanya domin inganta tashoshin jiragen ruwa a gabashi da yammacin kasar nan.

Gwamnatin tarayya dai ta yi alƙawarin inganta tashoshin jiragen ruwanta, ciki har da waɗanda ke birnin Lagos, cibiyar kasuwancin ƙasar nan, domin sauƙaƙa harkokin cinikayya

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...