Saurari premier Radio
24.7 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiJihohi da dama zasu fada cikin talauci idan gwamnatin ta kaddamar da...

Jihohi da dama zasu fada cikin talauci idan gwamnatin ta kaddamar da mafi karancin albashi na naira dubu 62.

Date:

Wani rahoton kungiyar gwamnoni ta Najeriya kan kudin shiga yayi gargadin cewa jihohi da dama zasu fada cikin talauci idan har gwamnati ta kaddamar da mafi karancin albashi na naira dubu 62.

Rahoton yace tuni jihohin Abia, Ekiti, Gombe, Katsina, Kogi, Imo, Oyo, Plateau, Sokoto, Yobe, da kuma Zamfara suka samu gibi a kasafin kudin 2022.

Rahoton yace idan kudin da jihohi ke kashewa kan ayyukan yau da kullum ya karu da kaso 50 cikin 100 to jihohi zasu fada cikin matsalar gibin kasafin kudi, inda yace jihohi 10 ne kacal zasu iya tsayawa da kafarsu cikin 36.

Jihohin kuwa sune Anambra,  Bayelsa, Borno, Ebonyi, Gombe, Imo, Jigawa, Kaduna da Lagos, sai Jihar Rivers da suka tabuka ta hanyar tara kudin shiga a shekarar 2022.

Rahoton ya bayyana jihar lagos a matsayin wadda tafi tara kudin shiga, inda a 2022 jihar ta samu naira triliyan 1 da biliyan 243 da miliyan 778, sannan ta kashe naira biliyan 621 da miliyan 43 wajen tafiyar da al’amuran yau da kullum.

Shima rahoton wata kungiya mai zaman kanta BudgetIt yace har kawo yanzu jihohi 15 cikin 36 sun gaza kaddamar da mafi karancin albashi na naira dubu 30.

Alumma dai na dakon bangaren zartasawa ya gabatarwa da majalisar daftarin mafi karancin albashin domin amincewa, duk da kungiyar kwadago ta nuna adawarta da naira dubu 62 da gwamnatin ke shirin gabatarwa a matsayin mafi karancin albashi.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...