Saurari premier Radio
29.1 C
Kano
Monday, July 22, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin tarayyaHukumar NLC da TUC sun baiwa hukumar kula da wutar lantarki wa'adi...

Hukumar NLC da TUC sun baiwa hukumar kula da wutar lantarki wa’adi don janye ƙarin farashi.

Date:

Kungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun bawa hukumar kula da hasken wutar lantarki ta kasa wa’adin ranar lahadi mai zuwa wato 12 ga watan Mayun da muke ciki, domin ta janye Karin farashin wutar lantarki a kasar nan ko su tsunduma yajin aikin sai Baba ta gani.

Sanarwar hakan na kunshe ne cikin wata takardar hadin gwiwa da kungiyoyin suka fitar mai kwannan watan 3 ga watan Mayun da muke ciki dauke da sa hannun Shugaban NLC Joe Ajaero da takwaran sa na TUC Festus Osifo, wadda suka aikewa da sakataren Gwamnatin tarayya da Ministan kwadago da makamashin wutar lantarkin da kuma kamfanin da ke kula da rarraba hasken wutar a kasar nan.

Takardar ta su ta bayyana cewa bayan matakin da suka dauka na bayyanawa wadanda abin ya shafa rashin amincewar su da Karin wutar lantarkin a ranar ma’aikata, tafiya yajin aikin shi ne mataki na gaba da zasu dauka matukar ba’a mayar da farashin yadda yake a baya ba.

Tun a ranar 3 ga watan Afrilun daya gabata ne dai ma’aikatar da ke kula da wutar lantarkin kasar nan tayi Karin kudin wutar daga naira 66 ya zuwa naira 225 ga wadanda suke amfani da layin da aka fi samun wutar na Band A, wadanda hukumar ta ce sune suke samun wutar ta kimanin awanni 20 a kullum.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...