Saurari premier Radio
29.1 C
Kano
Monday, July 22, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiHukumar lafiya ta duniya WHO ta tabbatar da sake ɓullar cutar kwalara...

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta tabbatar da sake ɓullar cutar kwalara a wasu ƙasashen na duniya.

Date:

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta tabbatar da sake ɓullar cutar kwalara a wasu ƙasashen nahiyar Afrika da gabashin Asiya sai Amurka da Turai da kuma yankin Mediterranean.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata mujallar da hukumar ke wallafawa.

Hukumar ta ce kimanin mutane dubu 195 ne suka harbu da wannan cuta a yankuna biya na duniya a tsakanin watan Janairu zuwa Mayu, inda a gabashin tekun Mediterranean kawai aka samu dubbu 98 daga ƙasashe 7.

A nan Najeriya ma cutar ta kwalara na ci gaba da bazuwa musamman a jihar Legas, inda zuwa shekaran jiya Asabar hukumomi suka ce an samu mutum 421 da ake zargin sun kamu da cutar yayin da kwamishinan lafiya na Legas ya tabbatar mutum 35 da na ɗauke da cutar.

Kwamishinan Lafiya na Legas, Akin Abayomi, ya tabbatar da mutuwar mutum 24 a faɗin jihar.

Hukumomin dai sun sake gargaɗi dangane da bazuwar wannan cuta zuwa wasu sassa na ƙasar nan.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...