Saurari premier Radio
29.1 C
Kano
Monday, July 22, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiGwamnatin tarayya ta hannun hukumar kwastam ta kasa ta kama wani jirgi...

Gwamnatin tarayya ta hannun hukumar kwastam ta kasa ta kama wani jirgi mallakin wani babban banki.

Date:

Gwamnatin tarayya ta hannun hukumar kwastam ta kasa ta kama wani jirgi mallaki wani babban banki a kasar nan bisa zargin kin biyan harajin shigo da jirgin Najeriya.

Wannan dai wata alama ce ta Yunkin gwamnatin na sa kafara wando guda da masu kananan jirage masu zaman kansu da basa biyan harajin biliyoyin naira.

Matakin na zuwa ne kasa da makwanni biyu da fara tantance rajistar mamallaka kananan jirage masu zaman kansu da hukumar ta yi a ranar 19 ga wannan wat ana Yuni wanda ake sa ran kammalawa 19 ga watan Yuli da muka shiga a yau.

Shirin tantancewar dai inji wata sanarwar hukum,ar, na da nufin gano masu hannu da shuni da suka sayo jiragen kuma suka shigo dasu batare da biyan harajin da yakamata ba.

Rahotanni sun ce, tuni hukumar kwastam ta nemi hukumar kula da jiragen sama Nigerian Civil Aviation Authority da hukumar dake kula da sararin samaniya Nigerian Airspace Management Agency da su soke lasisi zirga zirga na kananan jiragen masu zaman kansu, har sai hukumar ta kammala tantancewa.

Ko a ashekarar 2019 sai da hukumar ta samu sama da naira biliyan 2 sakamakon irin wannan aiki na tanatance kananan jirage da masu hannu da shuni ke amfani dasu.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...