Saurari premier Radio
23.8 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiGwamnatin Tarayya ta ƙaryata Rahotan da ake Yaɗawa cewa ta Miƙa tayin...

Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata Rahotan da ake Yaɗawa cewa ta Miƙa tayin Naira Dubu 105,000 a Matsayin Sabon Mafi ƙarancin Albashin.

Date:

Gwamnatin tarayya ta ƙaryata rahotan da ake yaɗawa cewa ta miƙa tayin Naira dubu 105,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikata a ƙasar nan.

Wannan dai na zuwa ne bayan da wasu labarai da ake yadawa a shaafukan sada zumunta ke cewa gwamantin  tarayya ta hannun ministan kudi Wale Edun ya miƙa tayin Naira 105,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikata a ƙasar nan.

Idan za’a iya tunawa dai ƙungiyoyin ƙwadagon kasar nan na NLC da TUC, sun janye yajin aikin da suka shiga bayan kulla yarjejeniyar sulhu a tsakaninsu da Gwamnatin Tarayya.

Sai dai bayan ganawar da ya yi da tawagar sulhun da Gwamnatin Tarayya ta wakilta, Shugaba Bola Tinubu ya bai wa Ministan Kuɗi wa’adin sa’o’i 48 domin cimma matsaya kan sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikata a ƙasar nan.

Dangane da hakan ne Ministan Kuɗin da tawagarsa suka ba da shawarar ƙayyade Naira 105,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikata.

Cikin wata sanarwar da mai magana da yawun Shugaban Kasa, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce babu ƙamshin gaskiya kan wannan batu.

Onanuga ya ce “ba gaskiya ba ne cewa Ministan Kuɗi ya ba da shawarar ƙayyade Naira 105,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...