Saurari premier Radio
23.5 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiGwamnatin Sokoto tayi martani ga mataimakin shugaban ƙasa.

Gwamnatin Sokoto tayi martani ga mataimakin shugaban ƙasa.

Date:

Gwamnatin Sakkwato ta yi martani ga Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima kan kalamansa game da zargin gwamnan jihar da neman tsige Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar.

Gwamnatin jihar ta ce ya kamata Shettima ya rika bincike ya tabbatar da gaskiya al’amari kafin ya yi tsokaci a kai.

Raddin na zuwa ne bayan gargadin da Shettima ya yi wa gwamnatin jihar cewa ta yi hattara da kujerar Sarkin Musulmi saboda muhimmacin matsayin basaraken abu ne da ya kamata duk Najeriya ta mutunta, ta girmama ta kuma kare ta.

Mataimkain shugaban kasar ya yi gargadin ne a taron tsaro da zaman lafiya na yankin Arewa maso yamma ranar Litinin a Jihar Katsina inda mataimakin gwamnan Sakkwato ya wakilci Gwamna Ahmad Aliyu.

Idan za a tuna Kungiyar Kare Hakkin Musulmi (MURIC) na zargin Gwamna Ahmad Aliyu da neman tsige Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Musulunci a Najeriya, kamar yadda gwamnan ya sauke wasu sarakunan gargaji 15 a kwanakin baya.

A martanin Gwamna Ahmad Aliyu ga Shettimma, ya bukaci mataimakin shuganan kasar ya rika bari sai ya san hakikanin gaskiyar al’amari, musamman wanda ya shafi kasa, kafin ya yi magana a kai.

A cikin sanarwar da kakakin gwamnan, Abubakar Bawa, ya sa wa hannu, ya ce, “Mun dauka mataimakin shguaban kasa zai yi hikimar tuntubar gwamna kafin ya yi magana kan lamarin a cikin jama’a.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...