Saurari premier Radio
24.9 C
Kano
Friday, April 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKiwon LafiyaGwamnatin Kano za ta tallafawa masu lalurar hakori 15,000 kyauta

Gwamnatin Kano za ta tallafawa masu lalurar hakori 15,000 kyauta

Date:

Gwamnatin Kano tace za ta tallafawa masu lalurar hakori 15,000 kyauta a masarautun jihar nan biyar.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da Jami’ar hulda da jama’a a ma’aikatar lafiya ta jiha Hadiza Namadi ta fitar ranar Juma’a.

Sanarwar ta ce gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana haka yayin kaddamar da shirin wayar da kan jama’a da kula da lafiyar baki kyauta a babban asibitin Tiga dake karamar hukumar Bebeji.

Ganduje wanda ya samu wakilcin Kwamishinan lafiya Aminu Ibrahim Tsanyawacya ce majinyata 3,000 daga kowacce masarauta ne za su amfana da shirin.

Kwamishinan ya yi kira ga al’umma musamman masu fama da ciwon hakora da su ziyarci cibiyar lafiya mafi kusa da su domin dubasu.

Ya kuma kara da cewa gwamnatin Kano ta ware miliyoyin nairori ta asusun kula da lafiya na jiha domin gudanar da aikin.

Tun da farko a nasa jawabin, babban sakataren asusun kula da lafiya na jihar Kano, Dakta Nura Idris, ya ce makasudin kafa asusun shi ne tallafawa gwamnatin jiha a fannin harkokin kiwon lafiya a fadin jihar.

A nasa jawabin, Mai Martaba Sarkin Rano, Alhaji Kabiru Muhammad Inuwa, wanda ya samu wakilcin Majidadin Rano Kuma Hakimin Bebeji, Alh. Tijjani Abdullahi kuki ya yabawa gwamnatin jiha bisa bullo da shirin wanda ya ce zai amfani jama’a matuka.

Shima da yake jawabi a wajen taron, shugaban karamar hukumar Bebeji, wanda sakataren karamar hukumar Alh. Hassan Usman ya Wakilta ya bayyana jin dadinsa ga gwamnan bisa zabar karamar hukumar domin gudanar da taron da kuma nada daya daga cikinsu a matsayin babban sakataren asusun kula da lafiya.

Latest stories

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Farashin Dizel ya koma 1000 a Najeriya

Rahotanni sun bayyana matatar mai ta Dangote ta sanar...

Related stories

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Farashin Dizel ya koma 1000 a Najeriya

Rahotanni sun bayyana matatar mai ta Dangote ta sanar...