Daruruwan shaguna rahotanni ke bayyana cewa sun kone kurmus, hadi da kayayyaki masu darajar miliyoyin naira, biyo bayan tashin gobara a babbar kasuwar Borno, wadda aka fi sani da kasuwar Litinin.
Wasu majiyoyi sun ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe 2 na daren jiya.
Zuwa yanzu, babu asarar rai da aka samu, yayinda yan kwana-kwana ke cigaba da aikin kashe wutar.
Har ila yau babu cikakken bayani game da musabbabin tashin ta, to amma, ba wannan ne karon farko da ake samun billar gobara a kasuwar ba.
Tuni dai gwamnan Borno, Farfesa Babagana Zulum ya ziyarci kasuwar, inda fusatattun matasa suka rika jifansa da duwatsu, sannan suna yi masa ihun ‘bama yi’.
Lamarin sai da ya kai jami’an tsaro ga harbe harben iska, da kuma jefa hayaki mai sa hawaye don tarwatsa matasan.