Saurari premier Radio
30.7 C
Kano
Monday, July 22, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiGargaɗi kan hasashen fuskantar mummunar ambaliyar ruwa a jihohi 19- Gwamnatin tarayya.

Gargaɗi kan hasashen fuskantar mummunar ambaliyar ruwa a jihohi 19- Gwamnatin tarayya.

Date:

Gwamnatin tarayya ta fitar da sanarwar gargaɗi kan hasashen fuskantar mummunar ambaliyar ruwa a jihohi 19, iftila’in da ake kyautata zaton zai fara aukuwa daga ƙarshen watan nan na Yuli.

Yayin ƙarin bayani kan hasashen masanan, Ministan kula da albarkatun ruwa da tsaftar muhalli na kasa Farfesa Joseph Utsev, ya bayyana matsalar toshewar magudanan ruwa a matsayin ɗaya daga cikin dalilan da za su haddasa ambaliyar yin muni da zarar manyan koguna sun tumbatsa.

Wasu daga cikin jihohin da ke fuskantar barazanar iftila’in ambaliyar dai sun haɗa da Kogi da Bayelsa da Jigawa da Kebbi da Taraba da Kaduna Cross River sai kuma Delta.

Mahukutan kasar sun shawarci jama’a da su yi tsaka-tsan-tsan gami da cutar kwalarar da ta ɓarke a baya bayanan, wadda ka iya yaɗuwa fiye da halin da ake ciki a wasu jihohi a dalilin ambaliyar da ake hasashen na tafe.

Duk da matakan da hukumomi ke dauka, amma duk shekara sai an samu iftila’in ambaliyar ruwan a wasu sassan kasar, lamarin da ke haifar da asarar rayuka da kuma dukiya mai yawa.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...