Saurari premier Radio
23.8 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin tarayyaFemi Falana yace babbar kotun tarayya ta kasa ba ta da hurumin...

Femi Falana yace babbar kotun tarayya ta kasa ba ta da hurumin sauraron kara da ta shafi batun masarautu.

Date:

Babban lauyan nan kuma mai fafutukar kare hakkin dan’adam Femi Falana yace babbar kotun tarayya ko kuma kotun masana’antu ta kasa basu da hurumin sauraron kara da ta shafi batun masarautu

A wata sanarwa da ya fitar a jiya Talata, Falana ya zargi kotunan tarayya dake shari’un masarautu a Kano da tsoma baki kan dambarwar masarautun da gangan duk kuwa da sun san basu da hurumin yin hakan.

Falana ya bada misalin Shari’ar Tukur da gwamnatin tsohuwar jihar Gongola inda kotun koli tace sarauta ba hakki ne na wajibi ga dan kasa ba, sannan baya cikin hakkokin da tsarin Mulki ya lissafta a matsayin na wajibi da kotuna zasu kare wa kowane dan Najeriya.

A yan kwanakin nan dai wata manyan kotunan tarayya biyu na Mai shari’a AM Liman da na mai Sharia Simon Amobeda sunce suna da hurumin sauraron kara da ta shafi masarutar Kano, duk kuwa da adawa da hakan lauyoyin gwamnatin Kano suka yi

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...