Saurari premier Radio
32.9 C
Kano
Saturday, April 20, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKiwon LafiyaFarashin wanka da bahaya yayi tashin gauron zabi a Kano

Farashin wanka da bahaya yayi tashin gauron zabi a Kano

Date:

Al’umma a jihar Kano na cigaba da kokawa bisa yadda farashin kudin wanka da bahaya ya karu a gidajen wanka dake fadin jihar nan.

A ‘yan kwankin nan dai masu gidajen wanka suka kara kudin da ake biya domin yin wanka ko zagayawa makewayi wanda hakan yasa mutanen dake amfani da guraren kokawa tare da neman dauki.

 

Wasu dake amfani da gidajen wankan da bahaya sunce kudaden da suke bayarwa don biyan bukatun su a duk lokacin da suka bukaci yin wanka ko turoso ya karu matuka ta yadda

wasu kan gwammace suyi bahaya a guraren da sahu ya dauke.

Sunce duk da samun kudin su bai karu ba amma hakan bai hana ma mallaka gidajen wankan kara kudi ba wanda hakan yasa wasu daga cikin su keyin fashin wankan a wasu lokutan.

Wasu masu gidan wanka sunce tsadar man fetur da rashin samun sa da kuma karancin wutar lantarki na daga cikin dalilan da yasa suka kara kudin da suke karba daga masu yin wanka da bahaya.

Shin da gaske ne mata a Kano basa wanka lokacin sanyi?

Abubakar Yusuf a unguwar Sharada cewa yayi a da suna biyan naira talatin kudin yin bahaya amma yanzu suna biyan naira saba’in yayin da kuma suke biyan naira dari da hamsin kudin wanka wanda ada suna biyan naira hamsin ne kawai.

Ya ce farashin yayi matukar yawa wanda hakan ke sanya su cikin mawuyacin hali.

Ya ce yana fatan masu gidajen wankan zasu rage kudin kasancewar galibin masu amfani da guraren basu da muhalli.
Isah Bello mazaunin unguwar hotoro dake kasuwanci a titin Zoo Road ya ce yana biyan naira tamanin domin yin turoso wanda ada ba haka yake ba.

Ya ce a hakan ma wasu gidajen wankan da bahaya sun rufe sakamakon dalilan da suke fada na rashin wutar lantarki da tsadar man fetur.

Ya ce idan har nan da wasu lokutan ba a rage kudin ba to basu da wani zabi da ya rage su rinka yin fashin wanka tare da yin bahaya a wasu guraren.

Hukumar CPC ta gano inda ake hada gurbataccen mai a Kano

Wani mai gidan wanka Alhaji Muhammad Nasiru Mai Sallah cewa yayi basu da wani zabi face su kara kudin duba da halin da ake ciki na tsadar abubuwan gudanar da gidan wankan.

Ya ce dole ce tasa suka kara kudin maimakon rufe gidajen wanda kuma hakan ka iya sawa wasu su shiga halin takura na rash in inda zasu kewaya musamman ma idan sun samu matsuwa.

Haramcin amfani da mutum-mutumi a Kano na nan daram – Hisbah
Alhaji Muhammad Nasiru Mai Sallah ya bukaci masu ruwa da tsaki da su kawo karshen karancin wutar lantarki da tsadar man fetur da ake fama da su wanda hakanne kadai zai sa su rage farashin wanka da na bahaya.

Latest stories

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Related stories

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Farashin Dizel ya koma 1000 a Najeriya

Rahotanni sun bayyana matatar mai ta Dangote ta sanar...