Muhammad Bello Dabai
Duk da janye gayyatar da gwamnatin Kano ta yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari domin bude wasu ayyuka da ta yi, da alama shugaban na nan tafe a ranar Litinin.
A wani sako mai harshen damo da mataimakin shugaban kan kafafen sada zumunta, Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya tabbatar da cewa Buhari na tafe a gobe Litinin.
Har ila yau, a wani sakon na daban, Bashir Ahmad yace duk wani mai shirin jifan shugaba Buhari a jihar Kano, to babu hannun Kanawa a ciki.
Da fari dai, gwamnatin Kano ta janye gayyatar da ta yi wa shugaban ne, biyo bayan jifan da tawagarsa ta sha a jihar Katsina.
Hakan dai ba zai rasa nasaba da batun sauyin takardun naira 200, 500 da kuma 1000 da gwamnatinsa ta toge akan sai ya tabbata ba.
Yanzu haka kwanaki 2 suka rage wa’adin dena karbar tsaffin takardun ya cika, wanda hakan ke nufin ga duk wanda bai sauya kudinsa ba, to zai tafka asara.
Lamarin a yanzu, ya haddasa tsayawar kasuwanci cak a wasu kasuwannin, sabida dakatar da tsaffin takardun da tuni wasu yan kasuwa suka yi, gabanin cikar wa’adin da babban bankin kasar CBN ya bayar.
