Saurari premier Radio
39.9 C
Kano
Wednesday, April 24, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDole gwamnati ta saukakawa mutane radadi kan batun sauyin kudi -Atiku

Dole gwamnati ta saukakawa mutane radadi kan batun sauyin kudi -Atiku

Date:

Hafsat Bello Bahara

 

Dan takarar shugaban kasa a jamiyyar PDP Alh. Atiku Abubakar yabi sahu dan takarar shugaban kasa na jamiyyar NNPP Sanata Rabiu Musa Kwankwaso wurin kira ga gwamnati ta sake duba kan wa’adin daina amfani da tsaffin kudi.

 

 

Atiku yace sauyin kudi a kasar nan da ma kasashen duniya ba sabon abu bane, sai dai wa’adin da aka saka na daina amfani da kudin zai sanya alumma cikin damuwa.

 

 

Atiku Abubakar ya fadi haka ne a safiyar yau Asabar a wani jawabi daya fitar a shafinsa na kafar Facebook.

 

 

Dan takarar shugaban kasa na jamiyyar PDP kenan Alh. Atiku Abubakar da yake kira ga gwamnatin tarayya ta sake duba wa’adin da ta sanya na daina amfani da tsaffin kudaden na naira 200 da 500 da kuma 1000 a kasar nan.

 

 

Atiku yace yan Najeriya masu kishi na nuna fargaba kan wannan manufa ta waadin sauyin kudin

 

 

Ya kara da cewa zasu cigaba da wayar da kan mutane kan amfani da kudi ta internet amma akwai bukatar a kara duba wa’adin.

Latest stories

Hukumar EFCC ta musalta zargin da ake mata na fara bincikar tsohon Gwamnan kogi.

Shugaban hukumar EFCC mai hukunta masu yiwa tattalin arziki...

Majalisar dokokin Kano ta nemi a dakatar da KEDCO kan yanke wuta.

Majalisar Dokokin jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar data...

Related stories

Hukumar EFCC ta musalta zargin da ake mata na fara bincikar tsohon Gwamnan kogi.

Shugaban hukumar EFCC mai hukunta masu yiwa tattalin arziki...

Majalisar dokokin Kano ta nemi a dakatar da KEDCO kan yanke wuta.

Majalisar Dokokin jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar data...