Saurari premier Radio
23.8 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiDan takarar shugaban ƙasa a tutar Jamiyyar PDP a zaben 2023 Atiku...

Dan takarar shugaban ƙasa a tutar Jamiyyar PDP a zaben 2023 Atiku Abubakar ya mikawa kotun ƙoli bukata

Date:

Dan takarar shugaban ƙasa a tutar Jamiyyar PDP a zaben 2023 Atiku Abubakar ya mikawa kotun ƙoli bukatar gabatar da sabbin shaidu a shari’ar da yake kalubalantar nasarar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

A kunshin bukatar da ya mika ta hannun lauyoyin sa karkashin jagorancin Chris Uche SAN, yace shaidar da yake kokarin gabatarwa zata tabbatar da zargin da yake na cewa takardun karatun da shugaba Tinubu ya baiwa hukumar zabe ta kasa INEC na jabu ne.

wadanda kuma da sune hukumar ta dogara wajen sahale masa tsayawa takara a zaben shugaban kasa na watan Fabrairun 2023.

Atiku yace abinda Shugaba Tinubu ya aikata, almundahana ne da karya, a don haka bai cancanci ya shugabanci Kasar nan ba.

Atikun na neman iznin kotun ne, domin gabatar mata da bayanan Karatun shugaba Bola Tinubu da ya karɓo a Jami’ar Chicago dake Kasar Amurka ranar 2 ga wannan watan.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...