Saurari premier Radio
33.9 C
Kano
Thursday, April 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBankuna Za Su Fara Bayar Da Katin Shaidar Zama Dan Kasa Ta...

Bankuna Za Su Fara Bayar Da Katin Shaidar Zama Dan Kasa Ta NIN.

Date:

Gwamnatin Tarayya ta ce a yanzu yan Najeriya za su iya neman bankunan kasuwancinsu su ba su katin cirar kudi wanda ya ke hade da katin shaidar zama dan kasa.

Yayin taron majalisar zartarwa ta tarayya ranar Laraba a Abuja, ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali Pantami, ya ce majalisar zartarwar ce ta amince da hakan.

Ya ce bankunan za su yi hakan ne ba tare da karawa al’umma ko kwabo ba.

Pantami, ya ce domin ragewa al’umma wahalhalu, hukumar samar ta lambar dan kasa, ta yi hadin gwiwa da babban bankin kasa, domin masu sha’awar samun katin.

Latest stories

Related stories