Saurari premier Radio
25.9 C
Kano
Monday, July 22, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiBabbar kotun Kano ta bukaci Hizbah ta bayyana a gabanta kan ƙarar...

Babbar kotun Kano ta bukaci Hizbah ta bayyana a gabanta kan ƙarar da Murja Kunya ta shigar.

Date:

A ci gaba da shari’ar da fitacciyar ’yar TikTok, Murja Ibrahim Kunya, ta yi karar hukumar Hisbah ta Jihar Kano, babbar kotun jihar ta bukaci Hukumar ta zo ta yi mata bayani kan wasu dokokinta masu kama da juna.

Babbar Kotun Kano da ke zamanta a Bompai ta umarci Hukumar Hisbah da ta turo mashawarcinta a bangaren shari’a domin yin bayanin yadda Hukumar take amfani da dokokin biyu masu kama da juna wadanda kuma suka fara aiki a rana daya.

Lauyoyin Murja Ibrahim Kunya na kalubantar dokar Hisbah da cewa ta saba wa Kudin Tsarin Mulkin Najeriya.

Kotun ta kuma umarci akawun Majalisar Dokokin Jihar Kano ya bayyana a gabanta domin yin cikakken bayanin dalilin da majalisar ta samar da dokokin masu kama da juna a rana daya.

Kotun ta nemi ya yi bayani dalla -dalla a kan shin ana amfani da Sashe na 10 na dokar Hisba ta KSHB law 2003 da wata dokar Mai taken KSHB law (4) 2003.

Haka kuma kotun ta umarci Hukumar Dab’i ta Jihar Kano da ta zo ta yi bayani game da takardar bangaren shari’a wacce aka yi amfani da ita wajen aiwatar da dokar Hukumar Hisbah.

Haka kuma Hukumar za ta bayar da bahasin yadda aka yi wannan doka ta zama cikakkiyar doka.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...