Saurari premier Radio
23.8 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiAnyi Karin kudin lantarki a Kaduna.

Anyi Karin kudin lantarki a Kaduna.

Date:

Kamfanin raba lantarki na Kaduna Electric ya kara kudin kowanne megawatt daya zuwa Naira 209.

Kamfanin ya ce karin kudin wutar ya shafi kwastomomin da ke amfani da layi na daya da na biyu ne kawai a safiyar Laraba.

Sanarwar da kakakin kamfanin, Abdul-Aziz Abdullahi, ya bayar ta ce karin kudin ya fara aiki tun daga shekaranjiya.

Karin kudin daga Naira 206 zuwa 209 ya zo kimanin wata guda bayan rage shi, sakammakon caccaka da kamfanonin raba wutar lantarki a kasar nan suka sha, bayan sun kara kudin saboda gwamnatin tarayya ta janye tallafi a bangaren.

A kwanan baya kamfanonin suka rage karin, bayan sanya baki da majalisar dokokin kasa ta yi.

Ana iya tuna cewa, majalisar dokokin ta soki tsarin da kamfanonin raba lantarkin suka bullo da shi na karkasa masu amfani da wutar zuwa rukuni hudu.

Band A shi ne layin da kamfanonin suka ba kwastomominsu tabbacin samun wutar lantarki ta akalla sa’a ashirin a kowace rana, yayin da sauran layukan kuma ba su da wannan tabbaci.

Sanata Ali Muhammad Ndume, ya ce wannan bambanci da kamfanonin suka kirkiro, ya ci karo da kundin tsarin mulkin kasa, wanda ya wajabta daidaita tsakanin ’yan Nijeriya.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...