Saurari premier Radio
30.7 C
Kano
Monday, July 22, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiAna sa ran jam'iyyar Conservative zata rasa madafun iko a zaɓen ƙasar...

Ana sa ran jam’iyyar Conservative zata rasa madafun iko a zaɓen ƙasar Birtaniya

Date:

Yau Alhamis ake zaben kasa baki daya na Birtaniya inda ake sa ran a karon farko cikin shekaru 14 jam’iyyar Conservative za ta rasa madafun iko, inda Firaminista Rishi Sunak zai yi sallama da ragamar tafiyar da kasar, sai dai ya ce har yanzu yana da fata.

Lokacin zaben na Birtaniya ana sa ran jam’iyyar Labour mai matsakaicin ra’ayin gaba-dai gaba-dai, za ta sake dawowa kan madafun ikon kasar, inda shugaban jam’iyyar, Keir Starmer, kana jagoran yan adawa zai zama sabon firaministan kasar.

Shi dai Keir Starmer ya zagaya kasar lokacin yakin neman zabe kuma zai zama firaminista na farko daga jam’iyyar Labour, tun bayan Gordon Brown wanda ya yi sallama da ragamar mulkin kasar ta Birtaniya a shekara ta 2010.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...